Lewati ke konten utama
Lirik lagu

Aure

Danmusa New Prince

Yace yar uwata
Tace dan uwana
Yace kinyo sifar larabawa

Ni naga ni naga auren soyayya
Yau andaura
Ina amarya chemata ga ango

Abakin kofa
Yazo ya bude fuska
Don kallonta

Yazam kaman al'ada
Shi agurinsa
Tunda aure babban bautane

In an raya
Kunga lada bansan qarshe ba
Babbar sunnah

Masu qaryar chewa anfasa to andaura
Kunyi qarya dama kunsaba da abun kunya
Ga amarya ga ango mukam munayin waka

Inda ankai auren soyayya sai mun leqa
Yanzu kundau sabon alqibla na hangen nesa
Inyace eh karda kiche a'a to dan Allah

Kaji ango kaima saurara saika duba
Tunda mata ance rauninsu ba qaryaba
Babu zagi ango ba duka mata taka

Tazamo ma tamkar aljannah che a gidanka
Yanzu rana dai tuni ta nuna yau munganta
Auyi aure auren soyayya bana fushiba

Keche yaga yaga yaga yaga ke ya gani
Kamar wasa
Kunsan lamarinsu

Yabi ciki haka ta jiki da jini
Ango da amarya burinsu sugansu suna
Rawa rawa irin juyin dan mazari

Yau ranar kuche to kusha shagalinku
Maza maza maza ango taho gida
Faka faka faka amarya ganinka takeso

Liki liki liki akache amaryaa
Biki biki biki zokuje daukar hoto da ango
Rana rana tazo shikenan gidan angonki

Zaki jeki chan zaki sauka Allah shike iko
Gani gani gani karsu miki amarya
Kinfi kinfi kinfi qarfin raini suji da Allah

Kafi kafi kafi ango kafi kaima
Kafi kafi kafi qarfin raini wallahi ango
Yace yar uwata

Tace dan uwana
Yace kinyo sifar larabawa
Yace yar uwata

Tace dan uwana
Yace kinyo sifar larabawa